Hukumar dake shirya gasar ƙwararrun ƙwallon ƙafa ta Najeriya, NPFL, ta sanar cewa za a fara gasar kakar bana ta 2026/27 a ranar 28 ga watan Augusta 2026.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa ranar Talata, a shafinta na Facebook ta ce za a ƙare gasar ne kuma ranar 28 ga Mayu 2027.
- Moroko ta doke Holand don kaiwa matakin ƙungiyoyi 16 a bugun fanareti
- Mai kallon gasar Wimbledon ya mika bukatar aure ga budurwar sa ana tsaka da wasa
Idan za a iya tunawa dai Ƙungiyar Enugu Rangers ce ta lashe gasar a bara wadda ya kawo yawan jimillar kofin NPFL da ta lashe zuwa 9.