Dillalan man fetur sun yi barazanar rufe gidajen mai a Najeriya idan Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin tilasta musu dokar kayyade farashi.
Sakataren Yada Labarai na Kasa na Kungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, ne ya yi wannan gargadi yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata.
Idan za a iya tunawa dai, Minista a Ma’akatar Man Fetur, Heineken Lokpobiri, a ranar Litinin, ya bukaci hukumar kula da albarkatun mai (NMDPRA), da ta kara sanya idanu kan abinda ya kwatanta da cin zarafin ’yan Najeriya ta hanyar sayar musu man fetur da tsada.
-
Mummunar ambaliyar ruwa ta halaka mutum 12 Accra
-
Arewa bata taba samun masoyi kamar Tinubu ba-Uba Sani
“A matsayin daya daga cikin bukatun cire hannun gwamnati a kayyade farashin man fetur, dole ne a bar kasuwa ta tabbatar da farashi. NMDPRA na da nauyi na musamman wajen hana cin ribar da ta wuce kima.” in ji shi.
Sai dai Kakakin kungiyar dillalan mai (IPMAN) ya musanta zargin cin ribar da ta wuce gona da iri, yana mai cewa ’yan kasuwa da yawa na fuskantar asara sabo da rage-ragen farashi da matatar mai ta Dangote ke yi cikin kwanakin nan.
Ukadike ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara binciken dalilin da ya sa farashin fetur ya yi tsada, sannan ta gyara matatun man ta, inda ya jaddada cewa ’yan kasuwa za su sayar da abin da suka saya.
Ukadike ya yi gargadin cewa, “’Yan kasuwa za su iya rufewa idan anyi kokarin tilasta aiwatar da dokar kayyade farashi-
Ba za ku ce min nawa zan sayar da kayana ba tare da kun san nawa na saye shi ba.”