Manyan ayyukan da gwamnatin Tinubu ta aiwatar wa yankin Arewa suna da yawa

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da ayyukan ci gaba a Arewacin Najeriya fiye da kowane shugaban ƙasa, yana mai cewa hakan zai ƙara masa yawan ƙuri’u a zaɓen shekarar 2027.

Yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE TV, Sani ya ce yana magana ne bisa alkaluma da bayanai, inda ya jaddada cewa babu wani shugaban ƙasa da ya yi wa yankin Arewa irin ayyukan da Tinubu ya yi cikin shekaru Uku da suka gabata.

Ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa Arewa ba za ta goyi bayan Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba, yana mai cewa shugaban zai samu ƙuri’u fiye da waɗanda ya samu a zaɓen 2023.

A cewarsa, gwamnatin tarayya ta kusa kammala aikin titin Abuja zuwa Kaduna bayan ta biya sama da naira biliyan 600 daga cikin kuɗin aikin da ya kai kusan naira biliyan 750.

Sani ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta fara ba da kuɗin aikin titin Kaduna zuwa Birnin Gwari da aka yi watsi da shi fiye da shekara 25, tare da tallafa wa Jihar Kaduna a fannin noma ta hanyar samar da takin zamani.

Haka kuma ya ce gwamnatin tarayya ta amince da kafa Jami’ar Kimiyya da Fasaha a Kudancin Kaduna, yayin da ta mayar da ɗaya daga cikin asibitocin jihar zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.

Gwamnatin ta kuma amince da bayar da aikin layin dogo a cikin birnin Kaduna da kudinsa ya kai naira tiriliyan ɗaya.

Gwamnan ya ce waɗannan ayyuka suna nuna ƙudirin gwamnatin tarayya na inganta rayuwar al’umma da bunƙasa ci gaban Arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *