Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA) sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa domin yaƙi da rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a gabanin zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya ce wayar da kan jama’a na da muhimmanci wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da ƙara yawan masu kaɗa ƙuri’a.
Ya ce inganta fasahar zaɓe kaɗai ba zai wadatar ba idan har jama’a ba su fahimci muhimmancin ƙuri’arsu ba.
- Oyebanji ne ya lashe zaɓen gwamna a Ekiti-INEC
- INEC zata yi amfani da Jami’an EFCC da ICPC a zaɓen Ekiti
- JADAWALIN ZAƁEN 2027 —INEC ta bayyana dalilan daukaka kara
Amupitan ya bayyana cewa yaɗuwar bayanan ƙarya da ƙarancin ilimin zaɓe na daga cikin manyan ƙalubalen da ke buƙatar haɗin gwiwar hukumomin biyu.
Ya buƙaci a riƙa gudanar da wayar da kan masu zaɓe a matakin al’umma, musamman matasa da mazauna karkara.
A nasa jawabin, Darakta Janar na NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya ce dimokuraɗiyya na dogara ne da ikon jama’a na zaɓar shugabanninsu.
Ya ce cibiyoyin NOA da ke faɗin ƙasar za su taimaka wajen isar da saƙonnin wayar da kai ga al’ummomi.
Issa-Onilu ya yi kira ga INEC da NOA su ƙara haɗa kai domin ƙarfafa ilimin dimokuraɗiyya, yaƙi da yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma ƙara yawan masu fitowa zaɓe a 2027.