Tawagar ƙwallon ƙafa ta Senegal ta fice daga Gasar Kofin Duniya bayan ta sha kashi a hannun Belgium da ci 3-2 a wasan zagaye na 32.
Senegal ce ta fara cin ƙwallaye biyu ba tare da an zura mata ko ɗaya ba, kuma ta ci gaba da jan ragamar wasan har zuwa mintuna na ƙarshe.
Sai dai Belgium ta yi nasarar farke ƙwallayen biyu kafin cikar lokacin wasa, lamarin da ya sa aka tafi ƙarin lokaci.
A ƙarin lokacin ne Belgium ta samu bugun fenariti, inda ta zura ƙwallo ta Uku, ta tabbatar da nasarar ta tare da samun tikitin zuwa zagayen ‘yan 16, yayin da Senegal ta yi bankwana da gasar.
A wani wasan kuma, tawagar Amurka ta samu nasarar doke Bosnia, lamarin da ya ba ta damar tsallakawa zuwa zagaye na gaba na gasar.
Kawo yanzu kasashen Amurka, Norway, Ingila, Brazil da Belgium sun samu tsallakawa zuwa zagaye na gaba.