Sabon dan wasan Chelsea, Palestra

Chelsea ta kammala daukan dan wasan baya na bangaren dama na kungiyar Atalanta, Marco Palestra, kan kudi kusan fam miliyan 47, ciki har da wasu tagomashi.

Dan shekaru 21, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru shida, da zabin karin shekara guda, shi ne na farko da ya zo tun bayan nada Xabi Alonso a matsayin kocin kungiyar.

A baya, an cimma yarjejeniyar Palestra ya koma tsohuwar kungiyar sa tun yana yaro, Inter Milan, amma Chelsea ta yi sauri ta zarce tayinta na farko na fam miliyan 43, kuma ta sanya albashi mai yawa, kamar yadda majiyoyi daga Italiya suka bayyana.

“Abubuwa da yawa ne suka sa na yarda na koma Chelsea, daya daga cikin manyan kungiyoyi a duniya,” in ji Palestra.

“Muna da ‘yan wasa masu hazaka da yawa a nan, kungiya da koci mai karfi Xabi.

“Ya yi magana da ni kan yadda yake son mu buga wasa, abin da ke da ban sha’awa, kuma na zaku naga mun fara fafatawa a gasar Firimiya.”

Palestra ya yi kakar da ta gabata a matsayin dan wasan aro a Cagliari kuma an zabe shi a matsayin dan bayan da ya fi kowa a Serie A.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *