Mataimakin Shugaban Ƙasa na Musamman a kan Al’amuran Jaridu, Abdulaziz Abdulaziz ya ce Gwamnati ta san da labarin hukumar bogi da ake zargin Adeniyi Adeyemi ya kafa tun ma kafin kafofin yaɗa labarai su fara yayatawa.
A wata hira da ya yi da Basheer Nuhu Masa, Malam Abdilaziz ya ce irin wannan abu ba sabo ba ne kuma bai takaitu ga Najeriya ba.
- ‘Sauye-sauyen tattalin arziki da tsaro sun fara haifar da ɗa mai idanu’ – Tinubu
- ‘Gwamnatina na bayar da goyon baya ga ‘yancin aikin jarida’ — Tinubu
A cewarsa, a ko’ina a duniya ana da irin waɗannan mutane masu fakar numfashi su aiwatar da mummunar aniyarsu ta zanba cikin aminci.
Abdul’aziz, wanda ya nuna rashin jin dadi da abun, ya ce tuni an fara bincike kan batun kuma za a yi abin da ya dace.
Sai dai Mataimakin na shugaban ƙasa na Musammana kan Al’amuran Jaridua ya ba da tabbacin cewa gwamnati ta koyi darasi sosai, domin daga yanzu dole a kara bibiyar ydaa abubuwa suke tafiya da tabbatar da matakai na aiki.