Ƙasar Masar ta doke Australia da ci 4-2 bayan bugun fanareti, inda za ta kara da Argentina a zagaye na 16 na gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
Da farko dai, an tashi ne ci 1-1 a cikin filin wasa.
-
Colombia ta fitar da Ghana a gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
-
Cape Verde ta girgiza duniya duk da ficewa daga gasar cin kofin duniya
Wannan shine karo na farko tun 1934 da Masar ta tsallaka zuwa zagaye na 16 a gasar Cin Kofin Duniya.
A yanzu, Masar ta zama ƙasa ta biyu ta Africa da ta kai zagaye na 16, bayan Morocco ta riga ta samu tikitinta a farkon makon bayan nasararta a kan Holand.
Ana sa ran ƙasashen biyu na Masar da Moroko su farantawa al’ummar Afirka rai ta hanyar kai wa wasan ƙarshe na gasar wadda a tarihi babu wata ƙasa daga Afirka da ta taba kaiwa.
