Azzedine Ounahi ya ci kwallaye biyu kafin Soufiane Rahimi ya ƙara ta uku domin fitar da mai masaukin baƙin gasar Cin Kofin Duniya, Kanada, da ci 3-0 a Houston.

Morocco ta zama ƙasa ta farko a Afirka da ta kai matakin kwata fainal a gasar Cin Kofin Duniya sau biyu a jere.

Atlas Lions yanzu suna da damar kai wa matakin wasan kusa da na ƙarshe na gasar Cin Kofin Duniya sau biyu a jere, idan sun doke Faransa ko kuma Paraguay a zagaye na gaba.

A shekarar 2022, Morocco ta ajiye tarihi, inda ta zama tawaga ta farko daga Africa da ta kai matakin kwata fainal a gasar Cin Kofin Duniya.

Idan Faransa ta doke Paraguay a wasan su na zagaye na 16, Moroko za ta samu damar ɗaukar fansa kan rashin da ta yi a wasan kusa da na ƙarshe a Qatar, a ranar Alhamis, a Boston.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *