Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya gargaɗi gidajen rediyo da talabijin da su guji yaɗa labaran ƙarya, yana mai cewa nasarar manyan zaɓuɓɓukan 2027 ta dogara ne kacokan a kan yadda kafofin yaɗa labarai suke gudanar da ayyukansu.
Yayin jawabinsa ranar Laraba, 8 ga Afrilu, 2026, a wurin Babban Taron Kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin na ƙasa (BON), shugaban ya jaddada cewa babbar barazanar da ke fuskantar zaɓe a yanzu ba hargitsi ba ne, face yaɗa bayanan bogi waɗanda ka iya rura wutar rikici.
- Yadda mahalarta Babban Taron APC suka ‘cika titunan’ Abuja
- Yadda sanarwar INEC kan tace rajistar masu zabe ta bar baya da kura
- INEC ta shiga tsaka mai wuya game da ADC
Amupitan na ganin bin Dokar Zaɓe abu ne da zai taimaka wa kafafen yaɗa labarai su zama masu nagarta.
Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai su kiyaye dokokin da suka shafi yaɗa ra’ayoyin siyasa, musamman bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar bayyana ra’ayoyinsu ba tare da nuna son kai ba.
Haka kuma Shugaban ya gargaɗi kafofin yaɗa labarai da su daina bari ana amfani da su wajen yin kalaman tunzura jama’a ko ƙabilanci ko nuna wariyar addini, wanda ka iya ruguza zaman lafiyar ƙasa.
Daga nan ya tuna wa gidajen yaɗa labaran cewa akwai dokar daina kamfen sa’o’i 24 kafin ranar zaɓe.
“Wannan lokacin an ware shi ne don masu jefa ƙuri’a su samu natsuwar yanke shawara ba tare da matsin lamba ko ruwan bayanan ƙarya ba”, inji shi.
Farfesa Amupitan ya nuna damuwa kan yadda gidajen rediyo na jihohi ke nuna goyon baya ga gwamnati mai ci, da kuma yadda sayar da lokaci da tsada ke hana ƙananan jam’iyyu damar tallata kansu.
A cewarsa, “Kafafen da kuke amfani da su wajen yaɗa labarai mallakin al’umma ne, don haka dole a yi amfani da su wajen kare gaskiya.”
Farfesa Amupitan ya tabbatar da cewa INEC a shirye take ta bayar da sahihan bayanai a kowane lokaci, kuma ya buƙaci kafofin yaɗa labarai su rinka duba shafukan hukumar na hukuma don guje wa yaɗa jita-jita.