Hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta kama wata mata ‘yar Najeriya-da-Biritaniya mai shekaru 67, Mrs Mary Barek, bisa zargin yunƙurin yin fataucin kilogiram 13 na hodar iblis (Cocaine) da aka ɓoye cikin ɓawon ayaba na bogi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, dake Lagos.
A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, “Bayan cikakken bincike kan jakunkunanta, an gano ƙunshin Hodar Iblis manya 31 da aka ƙunsa a ayaba, mai nauyin kilogiram 13.
-
Sojoji sun ceto mutane 6 daga hannun ‘yan bindiga a Borno
-
‘Yan Sanda sun ceto mata da ɗanta da masu garkuwa suka sace a Jihar Kwara
Ya ƙara da cewa, “A cikin bayanin ta, tsohuwar ta amsa cikakken mallakar Hodar Iblis din da aka kama.”
Babafemi ya ce an kama wacce ake zargin, wacce ke aiki a matsayin mai kula da marasa lafiya a Birtaniya, ranar Lahadi, 28 ga Yuni, yayin da take kokarin shiga jirgin Virgin Atlantic zuwa Landan.
Har wayau, Babafemi ya ce Shugaban ta NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami’an Hukumar kan jajircewa da suke yi wajen gudanar da ayyukansu da kuma wayar da kan al’umma da su keyi.