Wani jirgin ruwa na katako mai dauke da ɗalibai da ke dawowa daga rubuta jarrabawa ya nutse a tsakiyar Jamhuriyar Dimoukaraɗiyyar Congo, inda ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 20, kamar yadda hukumomi suka ce.
Jirgin ya nutse yayin da yake shiga inda kogin Sankuru da Kasai suka haɗu a jihar Kasai a ranar Juma’a, kamar yadda shaidu suka bayyana.
“Akwai waɗanda suka tsira 80 da gawarwaki 20,” in ji Francois Kabula, mai kula da yankin Ilebo a Jihar Kasai.
-
Ƙungiyoyin ‘yan tawaye sun kai hari kan sansanonin sojin Mali a sabbin hare-hare
-
Jagoran addnin Iran bai halarci shirye-shiryen binne mahifinsa ba
-
Sojoji sun ceto mutane 6 daga hannun ‘yan bindiga a Borno
Duk da haka, wani shaidar gani da ido mai suna, Tshikudi Jean, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa jirgin yana ɗauke da mutane fiye da 200.
Har wayau, Shugaban ƙungiyar farar hula ta Ilebo, Francois Malepo, ya bayyana cewa “Masu jirgin ruwa a DRC kawai bayan kuɗi suke, ba sa damuwa da rayuwar mutane.”
Hukumomi a ƙasar suna yawaita alaƙanta mutuwar mutane a jirgin ruwa kan zargin tafiya da dare, cunkoso a jiragen ruwa, da kuma rashin bin ƙa’idojin.