Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Donald Trump ya ce Alkalin wasan da ya baiwa da dan wasan Amurka Folarin Balogun jan kati a wasan da suka buga da Bosnia-Herzegovina abin tuhuma ne.

Trump, ya bayyana hakanne a fadar White House ranar Litinin kafin wasan Amurka na zagaye na 16 da Belgium.

Trump ya ce, “Wannan Alkali, wanda yake da alamar tuhuma idan kuka duba tarihin sa, ya yanke hukuncin da babu wanda ya amince da shi.

Balogun ne mafi kyawun dan wasan mu, ko daya daga cikin mafi kyawun ‘yan wasan mu, sannan ya ba shi Jan kati, ban san abin da hakan yake nufi ba… Eh, na bukaci FIFA ta sake duba lamarin.” Inji Trump

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta amince da bukatar Trump, inda ta ce bisa la’akari da kudiri na 27 na dokokin ta, aka janye dakatar da haramcin da aka yiwa dan wasan har sai bayan shekara guda.

Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA, ta soki matakin da FIFA ta dauka akan wannan batu, inda ta bayyana matakin a matsayin “tsantsar rashin adalci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *