Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) ta soki matakin FIFA na dakatar da aiwatar da haramcin wasa daya, na dan wasan gaban Amurka, Folarin Balogun, inda ta bayyana matakin a matsayin “rashin adalci wanda ba shi da tushe.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin yanar intanet, UEFA ta ce shawarar FIFA na janye dakatarwar da tayi wa dan wasan sai bayan shekara guda, tamkar ketare iyaka ne da raunana mutuncin gasar.
“Idan masu kula da doka ba sa tabbatar da bin dokoki, to mutuncin wasan yana cikin haɗari kuma darajar gasar na raguwa,” in ji UEFA.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai ta jaddada cewa kwallon kafa ta ginu ne akan dokoki da ke tabbatar da gaskiya da adalci, inda ta ce haramcin wasa daya na tilas bayan samun jan kati doka ce wadda ba za a iya yin watsi da ita ba.
-
Neymar ya sanar da yin murabus daga Brazil
-
Gasar Cin Kofin Duniya: Messi, Mbappe, Kane ko Haaland, wa zai lashe Takalmin Zinare?
A cewar UEFA, rashin aiwatar da dokoki bai daya, ka iya haifar da barazana ga makomar gasar kwallon kafa, domin zai haifar da misali marar kyau ga wasanni da ke tafe anan gaba.