Tottenham Hotspur ta sake karya tarihin sayen dan wasa da tsada bayan ta tabbatar da sayen dan wasan tsakiyar Newcastle, Sandro Tonali.
Kwanaki 4 kacal bayan sayen Mateus Fernandes kan fam miliyan 85, Spurs ta sake kara gaba, inda ta dauko Tonali a yarjejeniyar da aka ce ta kai ta fam miliyan 100.
-
Gasar Cin Kofin Duniya: Messi, Mbappe, Kane ko Haaland, wa zai lashe Takalmin Zinare?
-
Neymar ya sanar da yin murabus daga Brazil
“Na yi magana da Babban Kocin Tottenham na kusan tsawon sa’o’i 2 game da kungiyar, magoya baya, filin wasa da kuma salon kwallon mu. Kamar sihiri ne saboda na gane nan take cewa dole in sanya hannu ga kungiyar,” in ji Tonali.
Kungiyoyi irin su Arsenal, Manchester United da Manchester City duk sun yi zawarcin dan wasan.
