Hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta  ta ware kimanin naira biliyan 8 da miliyan 400 a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin gina  tituna.

Bayanan kasafin kuɗin sun nuna cewa an ware wa hukumar jimillar Naira biliyan 22 da miliyan 820, a kasafin kudin bana.

Kuma an tanadi sama da Naira Biliyan 21 domin ayyukan raya ƙasa, yayin da fiye da Naira Biliyan ɗaya aka ware domin gudanar da harkokin yau da kullum.

Daga cikin manyan ayyukan da aka ware wa kuɗi akwai gina  tituna a Jihar Ogun da kuma hanyoyin cikin gari a wasu yankunan Jihar Katsina da kuma hanyoyin cikin Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke garin Iyin a Jihar Ekiti.

Sannan an ware Miliyoyin Nairori domin samar da motocin ɗaukar  marasa lafiya da kayan aikin cibiyar kula da haƙori da fitilun hasken rana da kuma kayan tallafa wa mata da matasa a wasu sassan Jihar Katsina.

Sai dai masana da masu fafutukar tabbatar da gaskiya a harkokin kasafin kuɗi na bayyana damuwar su, kan ayyukan da aka ware wa hukumar da cewa ba sa cikin nauyin da doka ta ɗora mata.

Hukumar wadda aka kafa a watan Mayun a shekarar 2023 ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, an ba ta alhakin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, haɗa ilimin boko da na addini da kuma inganta koyar da sana’o’i ga almajirai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *