Cibiyar nazarin manufofi da dabaru ta Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru, ta aikawa Gbong Gwom Jos kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Plateau, Mai Martaba Da Jacob Gyang Buba, wasiƙar ban haƙuri.
Matakin ya biyo bayan rashin fahimtar da ta kunno kai, sakamakon wasu kalamai da Daraktan Cibiyar Farfesa Ayo Omotayo, ya yi a wata hira da gidan talabijin na Arise.
A cikin wata wasiƙa da ya aikewa Masarautar a ranar Litinin, Farfesa Omotayo ya wanke kansa da cewa, lokacin da yake amsa tambayoyi kan halin da ake ciki, ya alaƙanta harin da yan kabilar Berom bisa kuskure.
-
Hukumar kula da Almajirai ta ware Naira biliyan 8.4 don gina tituna
-
IPMAN: Sayen fetur kai tsaye daga matatar Ɗangote zai rage farashin lita a gidajen mai
Daraktan ya ce ba shi da wata boyayyiyar manufa ta ɗora alhakin kai wannan hari a wuyan ɗaukacin al’ummar Berom, sannan bai taba nufin cewa akwai wata rundunar mayakan sa-kai, ko ‘yan tawaye da ke da alaƙa da Masarautar ba.
Daraktan ya nemi afuwar Sarkin, tare da ban haƙuri ga Masarautar Berom sakamakon ɓacin rai da kalaman nasa suka haifar ga al’ummar ta.
A ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, 2026, Farfesa Ayo Omotayo ya bayyana wa gidan talabijin na Arise cewar yunkurin kai harin na da alaƙa da ƙungiyar “Berom militia.”
Ya ce cibiyar na fuskantar matsin lamba daga ƙungiyar, cewar sai ta biya diyyar gonakin kakannin su da aka yi amfani dasu wajen gina Cibiyar.
