Hukumomin tsaron Afirka ta Kudu sun kama mutum ɗari biyu a wani babban samame da suka kai kan masu haƙar ma’adinan zinariya ba bisa ƙa’ida ba a wani tsohon ramin ma’adinai da ke yammacin birnin Johannesburg.

Yawancin waɗanda aka kama ba su da takardun izinin zama a ƙasar, kuma jami’an tsaro sun ƙwace makamai da harsasai a yayin samamen.

An gudanar da samamen ne haɗin gwiwar ‘yan sanda da sojoji da jami’an tsaro masu zaman kansu. Matakin na daga cikin shirin da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya ƙaddamar a watan Fabrairu domin yaƙi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a wuraren da ake fama da rashin tsaro.

‘Yan sanda sun ce fiye da mutum 100 daga cikin waɗanda aka kama ‘yan ƙasar Lesotho ne da ba su da takardun zama, yayin da aka kuma kama wasu daga Mozambique da Zimbabwe, da kuma wasu ‘yan ƙasar Afirka ta Kudu. Gwamnati ta ce ƙungiyoyin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na da alaƙa da manyan laifuffuka kamar karɓar kuɗin fansa, kisan gilla da sauran ayyukan ta’addanci.

Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ya zama ruwan dare a Afirka ta Kudu, inda dubban mutane ke shiga tsofaffin ramukan ma’adinai domin neman zinariya da sauran ma’adanai cikin mawuyacin yanayi. Da dama daga cikinsu na fitowa ne daga ƙasashen maƙwabta sakamakon talauci da ƙarancin guraben ayyukan yi.

Wannan samame na zuwa ne yayin da gwamnatin Afirka ta Kudu ke ƙara tsaurara matakai kan baƙin haure da ba su da takardun izinin zama.

A baya-bayan nan, dubban baƙin haure sun fice daga ƙasar, bayan matsin lamba daga wasu ƙungiyoyin cikin gida da ke zargin baƙin hauren da kwace guraben ayyukan yi da ya kamata su kasance na ‘yan ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *