Majalisar Wakilai ta yi fatali da ƙudurin neman a gayyaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya yi bayani kan zargin rashin sakin kuɗaɗen ayyukan mazabu a faɗin ƙasar.
Ƙudurin, wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Aba ta kudu da arewa a jihar Abia, Alex Mascot Ikwechegh na jam’iyyar LP, ya gabatar, ya nemi Shugaban ƙasar ya bayyana gaban majalisar kan jinkirin da ake samu wajen samar da kuɗaɗen ayyukan mazaɓu.
- Majalisar Dattawan ta nesanta kanta dangane da hukumar da ake taƙaddama a kanta
- Haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba: An kama sama da mutum 200 a Afirka ta Kudu
Sai dai ƙudurin ya haifar da muhawara mai zafi a zauren majalisar, inda ɗan majalisar APC daga jihar Plateau, Yusuf Gagdi, ya nuna adawar ƙarara, yana mai ra’ayin babu wani dalili da zai kai ga gayyatar shugaban ƙasa.
Da yake yanke hukunci, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce buƙatar gayyatar Shugaba Tinubu ba ta cikin ainihin ƙudurin da aka gabatar, saboda haka ya bayyana ta a matsayin wadda ta saɓa da ƙa’idojin majalisar.
