Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta ƙaddamar da asusun amintattu na tsaron Arewacin Najeriya (NNSTF). 

Ƙungiyar ta naɗa tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Mahmud Yayale Ahmed, da tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), domin shugabancin hukumar amintattun asusun.

Yayin da yake jawabi a wurin taron ƙaddamarwar a Kaduna, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa samar da asusun wani babban mataki ne na magance ƙalubalen tsaron yankin ƙarƙashin tsari na bai ɗaya.

Ya bayyana cewa gwamnonin sun amince da ɗaukar wannan matakin ne tun a tarukansu na watan Disamba na 2025 da Maris na 2026 saboda yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara.

Mambobin hukumar sun haɗa da fitattun tsoffin jami’an tsaro da na gwamnati, da suka haɗa da tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Janar Umar Farouk Yahaya, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da tsohon Shugaban ‘Yan Sandan Ƙasa Usman Alkali Baba.

Har ila yau akwai tsoffin jami’an ‘yan sanda, kwastam, da ƙwararrun da masana daga jihohin yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *