Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar lII, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a yankin Arewacin kasar nan da su hada kai don yakar matsalar tsaro a yankin.

Da yake magana yayin taron haɗin gwiwa na gwamnoni da sarakunan gargajiya na Arewa a Kaduna, Sarkin Musulmin ya ce yankin na Arewa zai iya samun nasarar shawo kan matsalolin dake ci masa tuwo a kwarya ne kawai idan aka haɗa kai da yin aiki tare.

Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya kuma jaddada cewa dole ne yaƙi da rashin tsaro ya wuce batun banbance-banbancen addini da na ƙabila, inda ya bayyana cewa haɗin kai shi ne babban jigo da ƙarfin Arewa.

“Wannan wata madogara ce ta haɗin kai a gare mu. Ya fito ne daga dukkan jihohin Arewa 19 don yin aiki a matsayin jiki guda. Mun yi amanna cewa idan har kuna da haɗin kai, za ku fi mayar da hankali. Haɗin kai shi ne abu mafi mahimmanci,” in ji shi.

Sultan ɗin ya tunatar da cewa sarakunan gargajiya na Arewa sun daɗe suna yin kashedi game da tsatsauran ra’ayi mai ɗauke da makami, inda ya bayyana cewa tun a shekarar 2014 majalisar ta miƙa shawarwari kan yadda za a magance rashin tsaro ga Ƙungiyar Gwamnonin Arewa.

Ya nuna kyakkyawan fatan cewa tare da haɗin kai da jajircewa da taimakon Ubangiji, shiyyar za ta shawo kan ƙalubalen tsaron da ke fuskantarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *