Ofishin Kakakin Majalisar Wakilai na Ƙasa ya fayyace abin da ya faru a zaman majalisa na ranar Laraba, 8 ga Yuli, 2026, ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Abbas Tajudeen.

Wannan bayani ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da ake yi kan wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa Alexander Mascot Ikwechegh ya gabatar game da  kuɗaɗen gudanar da ayyukan raya ƙasa a ma’aikatun gwamnati.

Sanarwar ta bayyana cewa takaddamar ba ta shafi jigon ƙudirin ba, sai dai yadda ta keta sashe na 8 ƙaramin sashe na 1, na  dokar majalisar.

Sashen  ya tanadi cewa dole ne a miƙa kowane ƙudiri ga Shugaban Majalisa domin amincewa kafin a karanta shi.

Sai dai lokacin da ake gabatar da shi, an lura da ƙarin wasu buƙatu na daban waɗanda ba sa cikin takardar da aka amince da ita da farko.

Kakakin majalisar ya jaddada cewa ba a hana ɗan majalisar gabatar da ƙorafinsa ba, sai dai kawai an tsaya ne a kan ƙa’ida da dokokin da suka gina majalisar.

‘Daga ƙarshe, Shugaban Majalisar ya tura batun zuwa ga wani Kwamitin Wucin Gadi domin yin bincike na tsanaki da kuma kawo rahoto’, inji sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *