Rundunar ta ce sojojin Forward Operating Base (FOB) da ke Logomani a ƙaramar hukumar Ngala ta jihar Barno sun yi nasarar daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka kai.
A cewar sanarwar, duk da cewa maharan sun samu damar kutsawa wani ɓangare na katangar tsaron sansanin a farkon artabun, sojojin sun sake haɗa ƙarfi tare da kai farmakin martani wanda ya tilasta wa mayaƙan tserewa bayan sun yi musu mummunar illa.
- MDGIF ta jaddada muhimmancin bunƙasa kasuwar iskar gas a Najeriya
- Dole ne Arewa ta haɗa kai don yaƙi da Ta’addanci – Sultan
Sai dai rundunar ta bayyana cewa soja guda ya rasa ransa, a yayin fafatawar, yayin da wasu motocin yaƙi biyu da wasu kayan aikin soja suka lalace.
Rundunar ta tabbatar da cewa har yanzu sansanin na ƙarƙashin cikakken ikon sojoji, inda aka tura ƙarin dakaru tare da ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da tsaro.