Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, mutane shida da ake zargin mayaƙan ISWAP ne tare da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin Bataliya ta 192 a Borno.

Cikin wata sanarwa da Rundunar Operation haɗin Kai ta fitar a ranar Laraba 9 ga watan Yulin shekarar 2026, Rundunar ta ce ta gano wasu ƙarin bayanai game da ƙungiyar ta ISWAP.

Binciken farko da ɓangaren leƙen asiri na rundunar sojin ya gano na nuni  da cewa mayaƙan sun tsere ne daga wasu sansanonin ‘yan ta’adda da ke yankunan Guduf da Chikide, a tsaunukan Mandara na ƙaramar hukumar Gwoza.

Rundunar ta ce an samu kuɗi sama da Naira miliyan 1.54 da wayoyin salula guda biyu a hannunsu.

Rundunar ta kuma bayyana cewa ta kama wani da ake zargin mai kai wa ‘yan ta’adda magunguna ne a shingen bincike na Molai.

Sannan a yankin Tarmuwa na jihar Yobe an sake kama wani da tayoyin babura guda biyar da ake zargin zai kai wa ‘yan ta’adda ne.

Rundunar ta yi  gargaɗin cewa waɗanda ke baiwa yan ta’addar tallafi ko wata gudummawa su kuka da kansu, domin gujewa fuskantar hukunci mai tsanani.

A baya bayan nan dai rrundunar na ci  gaba da faɗaɗa hare-haren da take kaiwa a yankunan dake kan iyaka da tafkin chadi, tare da matse hanyoyin zirga-zirga ga masu tayar da ƙayar baya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *