Ziyarar Hafsan na da alaƙa da ƙarfafa wa dakarun Sojin gwiwar cigaba da gudanar da ayyukan su a yankin

Shugaban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shu’aibu, ya ce rundunar sojin Najeriya za ta cigaba da fadada ayyukan ta a yankin Kudu maso Gabashin ƙasar.

Yayin wata ziyarar aiki da ya kai sansanin sojin Nkwagu da ke Abakalikin jihar Ebonyi a ranar Alhamis, Waidi Shaibu, yace  manufar rundunar ta ginu ne akan ƙwarewa da jajircewa, ta fuskar tunkarar ƙalubalen tsaro a zamanance.

Yayin ganawar Hafsan da manyan jami’ai da sauran dakaru, Laftanar Janar Shaibu ya shaida musu cewar ziyarar ta sa, na da alaƙa da ƙarfafa musu gwiwar ayyukan sadaukarwar da suke yi a kullum, domin tabbatar da zaman lafiyar ƙasar.

 

Ya kuma buƙace su da su ci gaba da kasancewa cikin shiri, tare da cigaba da mutunta tsarin Mulki da dokokin da suka kafa aikin, da kuma mutunta haƙƙin dan-adam yayin da suke ci gaba da matsa lamba kan masu barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.

Ziyarar da Hafsan ya kai ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin ganewa idon sa shirin da rundunar ta yi, ta fuskar dabarun yaƙi, da ƙwarewar aiki da kuma walwala.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *