Babban Jagora na Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, Fasfoma Dokta Yohanna Buru, ya jagoranci tawagar malaman addinin Kirista zuwa ziyarar ta’aziyya ga iyalan matar Musulma da wasu mutane suka kashe ta a Maraban Jos, Jihar Kaduna.

 Fasfoma Buru ya nuna matsananciyar alhini game da wannan mummunan lamari, sannan kuma ya miƙa ta’aziyya ta gaske daga faɗin al’ummar Kirista zuwa ga iyalan da aka yi wa rasuwar.

Ya yi Allah wadai da kisan, inda ya bayyana cewa rayuwar kowane ɗan adam mai daraja ce kuma babu wani addini da yake goyon bayan tashin hankali ko kuma zubar da jinin maras laifi ba tare da bin doka ba.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin addini ko na ƙabila ba, da su rungumi zaman lafiya da ƙauna da gafartawa juna da kuma mutunta juna.

A cewarsa, ‘zaman tare cikin lumana da amsar addinin juna sune rukunai masu muhimmanci ga hadin kan kasa da ci gabanta’.

Fasfoma Buru ya bukaci shugabannin addinai da su ci gaba da wa’azin nuna tausayi da fahimtar juna, da tattaunawa, yayin da ya kwa ɗaitar da matasa da su yi watsi da ƙiyayya da tashin hankali, da kuma dukan taron jama’a na daukar doka a hannu.

Haka kuma, jagoran addinin ya yi kira ga jami’an tsaro da hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an yi adalci ta hanyoyin da doka ta tanada, tare da yin kira ga al’umma da su kwantar da hankulansu, su kuma guji ayyukan da za su iya ruruta wutar tarzoma.

Ya jaddada cewa Kiristoci da Musulmi sun daɗe suna rayuwa tare a matsayin maƙwabta tun kaka da kakanni, saboda haka ya kamata su ci gaba da ƙarfafa dankon abota, hadin kai, da mutunta juna.

Ya buƙaci daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai wajen inganta zaman lafiya, kare mutuncin dan adam, da kuma gina al’ummar da ake girmamawa tare da mutunta bambance-bambancen aƙida.

Iyalan mamaciyar sun nuna godiyarsu dangane da wannan ziyara da kuma saƙon nuna juyayi da aka nuna musu, inda suka bayyana hakan a matsayin babban mataki na nuna juyayi da kuma hadin kan addinai a wannan lokaci na alhini da suke ciki.

Idan za a iya tunawa, an ƙashe Mallama Ummulkhairi ne makonni biyu da suka gabata bayan da wasu mazauna yankin suka zarge ta da satar yaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *