Kotun Tsarin Mulkin ƙasar Senegal ta yi watsi da wata doka da aka gabatar wadda ke neman takaita ikon shugaban ƙasa tare da ƙara wa Majalisar Dokoki ƙarfi
Hukuncin da kotun ta yanke a ranar Alhamis shi ne sabon ci gaba a rikicin siyasa tsakanin Shugaban Ƙasa Bassirou Diomaye Faye da tsohon Firaministansa, Ousmane Sonko, wanda Faye ya sauke daga muƙaminsa a watan Mayu
Faye ne ya miƙa dokar gaban kotun domin tantance ta, inda kotun ta yanke cewa dokar “ta saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin ƙasar.”
- Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mu da Iran ta Rushe — Trump
- Wata mata ta haifi jariri tana barci a kasar Canada
- Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mu da Iran ta Rushe — Trump
Dokar ta tanadi hana shugaban ƙasa jagorantar wata jam’iyya ko ƙawancen jam’iyyu. Haka kuma, ta bai wa Majalisar Dokoki ikon gudanar da bincike kan wasu batutuwa
Gwamnatin ta nuna rashin amincewa da yadda aka gabatar da dokar, tana mai cewa an yi hakan ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa ba. Haka kuma, Shugaba Faye ya shirya gabatar da ita ga al’umma domin kada kuri’ar raba gardama
A halin yanzu, Ousmane Sonko ne ke jagorantar Majalisar Dokokin da ta amince da dokar. Shi ne kuma shugaban jam’iyyar Pastef, wadda ta gabatar da ƙudirin dokar, kuma ita ce jam’iyyar da Shugaba Faye ke cikinta.
A makon da ya gabata, Faye ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai kafa sabuwar jam’iyyarsa ta siyasa.
Rikicin na zuwa ne yayin da ƙasar ke shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a shekarar 2027, wanda ake sa ran zai zama gwaji na farko da zai nuna ƙarfin siyasar ɓangarorin biyu.
Ana kuma ganin cewa kafa sabuwar jam’iyyar shugaban ƙasa na iya sauya tsarin siyasar Senegal matuƙa, tare da sake fasalta ƙawancen siyasa a cikin gwamnatin ƙasar.