Zakara mai kare kambun Gasar Wimbledon, Jannik Sinner ya kawo ƙarshen ƙokarin Novak Djokovic na lashe taken Grand Slam na 25 a tarihi, yayinda ya doke shi da ci 6-4 6-4 6-4 a ranar Juma’a, don buga wasan ƙarshe na Wimbledon da Alexander Zverev.
“Buga wannan wasa tare da Novak ya na da matuƙar muhimmanci a gare ni,” in ji Sinner.
“Har yanzu Novak abin koyi ne gare ku, har ma ga sabbin ‘yan wasa. Abin da yake yi abin mamaki ne.”
-
‘Idan akwai wanda ya kamata ya ji tsoro, shi ne Faransa’ – in ji Yamal
-
Gasar Cin Kofin Mata na Afirka: Madugu ya gayyaci Ajibade da Oshoala
-
Tennis: Zverev ya kawo karshen burin Fery na buga wasan ƙarshe na Wimbledon 2026
Kafin wannan wasa, lamba na 2 a duniya, Alexander Zverev ya kawo ƙarshen mafarkin ɗan Birtaniya Arthur Fery da ci 7-6(0) 6-2 6-4, don zama ɗan ƙasar Jamus na farko da ya kai wasan ƙarshe na maza tun bayan Boris Becker a 1995.
Sinner zai nemi ya lashe taken Grand Slam na 5 a ranar Lahadi yayin da zai kara da Zverev a wasan ƙarshe.
Ga Djokovic kuwa, wannan shine kashi na 5 a wasanni 6 na kwata fainal da yake shan kaye a ƙoƙarinsa na ƙara lashe taken Grand Slam, inda lokaci ke ƙokarin ƙure masa kan burinsa na zama wanda ya fi kowa lashe kofuna a gasar Tennis.
