Mia-Motley firaministar Barbados

Firaministar Barbados, Mia Mottley, ta yi watsi da iƙirarin da wata ‘yar majalisar Birtaniya ta yi cewa tsoffin ƙasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka su biya ta kuɗin irin jarin da ta zuba a cikinsu

Da take magana a ranar Alhamis, Mottley ta bayyana wannan ra’ayi a matsayin “marar hankali”, tana mai cewa ba zai yiwu a nemi waɗanda aka zalunta su biya masu zaluncin da aka yi musu ba.

Mottley ta yi wannan jawabi ne bayan tsohuwar Ministar Cikin Gida ta Birtaniya, Suella Braverman, wadda yanzu ke cikin jam’iyyar Reform UK mai adawa da yawan shige da fice, ta wallafa a shafinta na X cewa Daular Birtaniya ta yi alheri mai yawa ga duniya.

Braverman ta yi wannan furuci ne bayan wata ‘yar majalisar dokokin Birtaniya ta bayyana cewa ƙasar Jamaica na shirin gabatar da buƙatar neman diyyar bautar da aka yi wa kakanninta daga Birtaniya a ƙarshen wannan shekara.

Mottley ta yi waɗannan kalamai ne yayin taron manema labarai bayan kammala taron shugabannin ƙungiyar ƙasashen Caribbean (CARICOM), wanda aka gudanar a ƙasar St. Lucia

A taron, shugabannin sun tattauna batutuwa da suka haɗa da neman diyya kan bautar da aka yi wa ‘yan Afirka a zamanin cinikin bayi

A watan da ya gabata, Mottley ta jagoranci wani ƙaramin kwamitin shugabannin Caribbean da suka ƙaddamar da sabon kundin manufofi na neman diyya kan bautar da aka yi wa bayi, a wani taro da aka gudanar a ƙasar Ghana.

Tun a shekarar 2021, Barbados ƙarƙashin jagorancin Mottley ta yanke alaƙarta da Sarauniya Elizabeth ta II, inda ta daina kasancewa ƙasa mai tsarin mulkin sarauta ƙarƙashin Birtaniya.

A cikin ‘yan shekarun nan, gwamnatin Birtaniya ta ci gaba da jaddada cewa ba za ta biya diyya kan bautar da aka yi wa bayi ba.

Sai dai shugabannin ƙasashen Caribbean na ci gaba da neman Birtaniya ta ba da uzuri a hukumance tare da ɗaukar wasu matakai na gyara, ciki har da sassauta ko goge basussukan da ake bin ƙasashensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *