Yanayin zafi ya haifar da matsananciyar bukatar wutar lantarki a Amurka

Adadin wutar lantarki da ake samarwa a Amurka ya kafa sabon tarihi a makon da ya gabata, biyo bayan tsananin zafin da aka fuskanta a sassa da dama na ƙasar, wanda ya janyo ƙaruwar amfani da na’urorin sanyaya daki (AC).

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce bayanin na kunshe ne cikin wata kiddiga da Hukumar samar da lantarki ta Edison Electric Institute (EEI) ta fitar a wannan makon.

Hukumar ta bayyana cewa, ta samar da wutar lantarki da ta kai gigawatt-hour (GWh) 100,996 a makon da ya ƙare ranar 4 ga watan Yuli, adadin da ya zarce tarihin amfani da wutar lantarki da aka kafa a baya na GWh 99,445 a watan Yulin shekarar 2022.

A cikin mako 52 da suka gabata, jimillar wutar lantarki da Amurka ta samar ta kai miliyan 4.35 GWh, wanda hakan ke nuna ƙaruwar kashi 2.3% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

“Domin biyan buƙatun da ke ƙaruwa, da kuma tabbatar da jurewar hanyoyin rarraba wutar a matsanancin yanayi, akwai buƙatar ci gaba da zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa na makamashi a Amurka,” in ji Shugaban EEI, Drew Maloney.

A bayan bayan nan Amurka da sauran kasashe dake nahiyar Turai na fuskantar tsananin zafi a tarihi, inda aka samu mutuwar mutane sama da ɗari, matakin da ya haifar da matsananciyar buƙatar lantarki domin sanyaya matsugunai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *