Argentina za ta buga da Ingila don neman gurbin shiga wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
Ƙwallayen da Julian Alvarez da Lautaro Martinez suka ci bayan ƙarin lokaci sune suka baiwa Argentina nasarar ci 3-1 a kan Switzerland wadda ta ƙarkare wasan da ‘yan wasa goma.
Alexis Mac Allister ne ya fara ci wa Argentina ƙwallo da wuri, kafin Dan Ndoye ya farke wa tawagarsa ƙwallo kafin cika minti 60.
-
Najeriya ta samu tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya na mata ‘yan ƙasa da shekaru 17 na 2026
-
Zadok Yohanna ya shiga cikin ‘yan takara 100 na kyautar Golden Boy ta 2026
-
El-kanemi Warriors ta lashe Gasar Shugaban Kasa ta Tarayya ta Maza bayan doke Ikorodu
Switzerland ta yi tsayin daka don kare mutuncinta har aka tafi ƙarin lokaci, yayinda ake shirin zuwa bugun fenareti, Alvarez da Martinez suka ci ƙwallo biyu a cikin minti tara don kai Argentina wasan kusa da na ƙarshe.
Ga Switzerland, tarihi ne ya sake maimaitawa da Argentina.
Karo na ƙarshe da suka haɗu a Gasar Cin Kofin Duniya shi ne a zagayen 16 na 2014, inda Argentina ta doke ta da ci 1-0 a ƙarin lokaci da kwallon Angel Di Maria a minti na 118.