Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke wata ‘yar Afirka ta Kudu mai suna Will Jessica Ann, mai shekara 38, bisa zargin safarar iblis mai nauyin kilogram 5.75 a filin jirgin saman a Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ann  ta ɓoye hodar iblis guda 14 a cikin kayanta, inda ta yi amfani da ɗanta mai shekara uku a matsayin wata hanya ta kauce wa tsauraran binciken jami’an tsaro.

An kama matar ne ranar 6 ga watan Yulin 2026, yayin da take shigowa Najeriya daga Doha ta cikin jirgin Qatar Airways mai lamba QR 1433.

Hukumar ta bayyana cewa da farko matar ta musanta mallakar jakunkunan da aka ajiye a jirgi, amma bayan jami’an NDLEA sun gano cewa alamomin jakunkunan sun yi daidai da takardun kayanta, sai ta amince cewa nata ne.

Binciken Sirri na NDLEA ya nuna cewa matar na da alaƙa da wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasa da ƙasa tare da abokin zamanta, Jan Coenraad De Jager, wanda ake zargi da safarar ƙwayoyi tsakanin Cambodia da Afirka ta Kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *