Sojojin Bataliya ta 65 ta Rundunar Sojin Najeriya sun tare wata mota da ke ɗauke da manyan miyagun ƙwayoyi a kan hanyar gabar teku ta Lagos zuwa Calabar, bayan samun sahihan bayanan sirri daga wata majiya mai inganci.
A cewar Rundunar Sojin Najeriya, an gudanar da samamen ne a ranar 9 ga Yuli, 2026, inda aka samu nasarar kama motar tare da cafke direbanta.
Binciken farko ya nuna cewa ana jigilar miyagun ƙwayoyin ne zuwa yankin Berger da ke Jihar Lagos.
- NDLEA ta cafke ‘yar Afirka ta Kudu da ɗanta mai shekara 3 bisa zargin safarar hodar iblis
- Gwamnatin tarayya ta ƙara kuɗin rajistar jarabawar WAEC da NECO
- Rushewar ginin Majalisar Dokokin Gombe: Mutum ɗaya ya mutu, bakwai sun jikkata
Sai dai wanda ake zargin ya ƙasa bayar da gamsasshen bayani kan mai mallakar ƙwayoyin ko kuma wanda za a kai wa su.
Rundunar ta ce bisa ƙa’idojin aiki, an miƙa wanda ake zargin tare da miyagun ƙwayoyin da aka ƙwato ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Hedikwatar Jihar Lagos, domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.
Da yake martani kan nasarar aikin, Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya ta 81, Manjo Janar Adebayo Babalola, ya yaba wa sojojin bisa jajircewarsu, ƙwarewarsu da kuma ingancin aikin da suka gudanar.
Ya kuma buƙaci sojojin da su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan tsaro domin hana masu safarar miyagun ƙwayoyi da sauran masu aikata laifuka samun damar gudanar da ayyukansu a yankin da Rundunar ta 81 ke da alhakin tsaro.