Farashin danyen mai na Brent, wanda shi ne babban ma’aunin farashin mai na duniya, ya ƙaru da fiye da kashi 4 cikin ɗari a ranar Litinin yayin da Amurka da Iran suka yi musayar hare-hare a cikin rikicin da ke ƙara ƙamari kan ikon sarrafa mashigin Ruwan Hurmuz.
Ya zuwa ƙarfe 08:00 na safe agogon GMT, ɗanyen mai nau’in Brent ya kai dala $78.82 kan kowace ganga, wanda shi ne mafi girman farashi tun ranar 22 ga Yuni.
Rundunar Sojin Amurka (CENTCOM) ta bayyana a ranar Lahadi cewa ta kai hare-hare da dama kan Iran domin rage ƙarfin da take da shi na kai hari ga jiragen ruwa da ke bi ta Mashigin Hormuz.
Wannan ya biyo bayan wasu hare-hare da Amurka ta kai kan ɗaruruwan wurare a cikin Iran.
- Tsohon Sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya rasu
- Ƙasar Iran ta rufe Mashigar Hurmuz har sai abinda hali yayi
- Firaministar Barbados ta yi watsi da iIƙirarin cewa tsoffin mallakan Birtaniya su biya ta kuɗin zuba jarin da ta yi
Amurka ta ce ta ƙaddamar da waɗannan hare-haren ne bayan ta zargi dakarun Iran da kai hari “a fili” kan jirgin dakon kaya mai tutar Cyprus mai suna MV GFS Galaxy, yayin da yake wucewa ta mashigin.
A martanin da ta mayar, Ƙasar Iran ta ce ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa (drones) kan ƙasashen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Qatar da Kuwait da Oman da Bahrain.
Hukumar kula da Mashigin Tekun Fasha ta Iran ta sake jaddada cewa duk wani jirgin ruwa da zai bi ta Mashigin Hormuz ba tare da amfani da hanyar da Iran ta amince da ita ba, ba zai kasance ƙarƙashin tabbacin tsaron wucewa ba.