Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya (Comptroller-General), Bashir Adeniyi, Najeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 34 sakamakon rangwamen harajin shigo da kaya
Adeniyi ya bayyana hakan ne a yayin zaman bincike da Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin Kuɗi ya gudanar a ranar Litinin.
Ya ce takardun keɓance biyan harajin kwastam (Import Duty Exemption Certificates) da Gwamnatin Tarayya ta amince da su kan kayayyaki da na’urori sun kai darajar Naira tiriliyan 34.
- Sojoji sun kama masu yi wa ‘ yan bindiga safarar makamai daga Jos
- Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da ya hana INEC amincewa da taron majalisar jihohi na jam’iyyar ADC
- ‘Yan Sandan Abuja sun gurfanar da mutum 3 gaban Kotu kan zargin kisan kai
A cewarsa, yawan bayar da takardun keɓance harajin shigo da kaya ya rage yawan kuɗaɗen shiga na ƙasa.
Ya kuma ce matakan manufofin kuɗi da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka suna da tasiri mai kyau da kuma mara kyau ga ikon Hukumar Kwastam wajen tara kuɗaɗen shiga.
“Sauran rangwamen da gwamnati ta amince da su sun haɗa da shigo da kayan amfani da iskar gas da aka matse (CNG), motocin lantarki da na haɗaɗɗen makamashi (hybrid), kayan aikin asibiti da kayan jinya, injinan masana’antu da kayan aikin samarwa, da kuma shirye-shiryen shigo da abinci don rage matsin tattalin arziki.” Inji shi
A shekarar 2025, Hukumar Kwastam ta Najeriya ta samu kuɗaɗen shiga da suka kai Naira tiriliyan 7.28.