Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta harba makamai masu linzami zuwa ƙasar Saudiyya bayan ta zargi masarautar da kai hari ta sama kan filin jirgin sama da ke ƙarƙashin ikonta a ranar Litinin
Wannan ya kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta da ta ɗauki kusan shekaru huɗu tsakanin Saudiyya da ƙungiyar Houthi mai samun goyon bayan Iran.
Kakakin rundunar haɗin gwiwar sojojin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ya bayyana a shafinsa na X cewa, Saudiyya ta yi nasarar kakkabo makamai masu linzamin da “ƙungiyar ta’addanci ta Houthi ta harba zuwa yankin kudancin ƙasar.
- Abubuwan ban-mamaki 5 game da Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani
- Hurmuz zai ci gaba da kasancewa a bude duk da barazanar Iran – Trump
- An yanke wa shugaban RSF hukuncin kisa ba tare da ya bayyana a kotu ba
Shi kuwa kakakin rundunar Houthi, Yahya Saree, ya ce sun kai hari ne kan filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Abha, babban birnin wani yanki mai tsaunuka a kudancin Saudiyya da ke iyaka da Yemen, inda mutane da dama ke zuwa domin gujewa tsananin zafin bazara.
Wannan shi ne karo na farko da Houthi ta sanar da kai hari kan Saudiyya tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Maris na shekarar 2022, bayan hare-haren da ƙungiyar ta kai kan cibiyoyin makamashi na Saudiyya.
Rikicin da ya ɓarke a ranar Litinin ya haifar da fargabar sake dawowar yaƙi a kan iyakar kudancin Saudiyya, bayan da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami da Iran ta kai kan yankunan gabashin Saudiyya da birnin Riyadh suka ragu sakamakon yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Afrilu.