Hukumar ƙwallon ƙafa ta Guinea ta bukaci Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, CAF, ta canza wurin buga wasan neman tikitin shiga Gasar Cin Kofin nahiyar Afirka, AFCON, ta 2027 da Afirka ta Kudu zuwa wani wuri mai na daban saboda damuwar rashin tsaro.

A cewar rahotanni, Guinea ta bayyana cewa zanga-zangar adawa da bakin haure da ke gudana a Afirka ta kudu shine dalilin bukatar, inda ta bayyana damuwa kan tsaron ‘yan wasansu, jami’ai da kuma magoya bayan da za su je kasar.

Tuni dai hukumar ta Guinea ta riga ta miƙa buƙatar ga CAF a hukumance, inda take jiran amsa daga Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar.

Wasan neman gurbin shiga gasar AFCON ta 2027 ana sa ran zai kasance ɗaya daga cikin manyan wasanni, saboda duka ƙasashe biyu suna son samun tikitin shiga gasar.

A halin yanzu CAF bata fitar da wata sanarwa ba kan buƙatar Guinea. Har yanzu ba a tabbatar ko wasan zai kasance a Afirka ta Kudu ko za a mayar da shi wani wuri ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *