Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, tare da wasu manyan baƙi, sun halarci gasar tseren dawakai ta (Renewed Hope) ta yammacin Afrika karo na biyu da aka gudanar a ranar 11 ga Yulin 2026 a birnin Kaduna.

Taron ya haɗa manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan da maƙwabtan ƙasashen Yammacin Afirka, inda aka gudanar da gasar cikin yanayi na murna da nuna al’adun gargajiya da suka shafi kiwon dawakai da wasannin tserensu.

An shirya gasar ne domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka, bunƙasa harkokin wasanni da yawon buɗe ido, tare da nuna muhimmancin al’adun gargajiya wajen haɓaka tattalin arziki da haɗin kan al’umma.

Hoto daga wajen taron ya nuna Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, tare da sauran manyan baƙi yayin da suke halartar bikin, wanda Adnan Sulaiman na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Ƙasa (FMINO) ya ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *