Ɗaya daga cikin hafsoshin sojin Iran, Janar Naqdi, ya bayyana cewa idan har aka ci gaba da yaƙin, hakan zai kai ga ɓarkewar yaƙin duniya, kuma Iran za ta tabbatar da hakan ta faru.

Manjo Janar ɗin, a wani shirin talabijin, ya fito fili ya bayyana cewa har yanzu Iran tana da iko da ƙwarewar da za ta iya ƙera ƙarin makamai masu linzami, waɗanda wasu daga cikin manya da na gaba-gaba cikinsu ba a riga an yi amfani da su ba har yanzu.

A gefe guda kuma, Kakakin Majalisar Iran, Ghalibaf, ya bayyana cewa an mayar da mashigin ruwa na Strait of Hormuz zuwa yanayin lokacin yaki.

Kuma ya ƙara da cewa babu wani jirgin dakon mai da zai wuce ba tare da izinin Iran ba.

Ya kuma yi barazanar harba bindiga kai tsaye kan duk wani jirgin dakon mai da zai yi ƙoƙarin ƙauce wa dakarun sojan ruwan na Iran.

Rundunar IRGC a cikin wata sanarwa ta yi kira ga ɗaukacin mazauna duniya da su riƙa karɓar bayanai ne kawai daga rundunar sojan ruwan Iran dangane da halin da mashigin ruwan na Strait of Hormuz yake ciki.

Sun ƙara da cewa, babu wata magana da ta fito daga bakin Trump da ke da wata ƙima ko amfani a game da wannan batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *