Zakaran gasar kasar Scotland, Celtic, ta miƙa wa ɗan wasan gaba na Najeriya Kelechi Iheanacho tayin sabon kwantaragin shekaru biyu, bayan karewar kwantaragin sa na baya bayan nan.
An ce sabuwar kwangilar ta haɗa da albashin Fam dubu 35 duk mako, tare da kyaututtuka dangane da ƙwazon sa da ya kai Fam dubu 780 a tsawon shekaru biyun.
Wannan tayin ya zo ne bayan kyakkyawarbkakar da ɗan wasan Super Eagles din ya samu, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Celtic lashe gasar Scottish Premiership ta 2025/2026.
- Za mu buga mafi kyawun salon wasa akan Argentina da Messi – Tuchel
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Halarci Gasar Tseren Dawakai a Kaduna
- Spaniya ta kai wasan karshe na Cin Kofin Duniya bayan doke Faransa 2-0
Iheanacho ya zura kwallaye 7 a gasar, kuma gudunmawar sa ta kasance mai mahimmanci, yayin da Celtic ta sake lashe wani kofin gasar.
Ya samu yabo daga magoya baya da ma’aikatan horarwa, lamarin da ya sa zakaran Scotland ta fara tattaunawa da shi kan sabuwar kwangila.
Ana sa ran sanarwa a hukumance kan makomar Iheanacho da zarar an kammala tattaunawa tsakanin ɗan wasan da ƙungiyar.