Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ce babbar matsalar ilimi a Najeriya ba yawan masu rajista ba ce, illa rashin damar da yara ke samu na ci gaba da karatu daga firamare zuwa ƙaramar sakandare.

A jawabin da ya gabatar a Taron Shekara na 2026 na Ƙungiyar Masu Rahoton Ilimi ta Najeriya (ECAN) a Abuja, Alausa ya bayyana cewa duk da kusan yara miliyan 25 da ke makarantun firamare, kimanin miliyan biyar ne kawai ke ci gaba zuwa ƙaramar sakandare.

Ya danganta hakan da ƙarancin makarantu, yana mai cewa Najeriya na da kusan makarantun firamare dubu 90, amma ƙaramar sakandare kusan dubu 16 kacal, abin da ya nuna akwai babban giɓi wajen samar da damar ci gaba da karatu.

Ministan ya kuma buƙaci ‘yan jarida su yi amfani da bayanan da ke cikin tsarin Tsarin Kula da Bayanai da Gudanar da Bayanai kan Ilimi na Najeriya (NEDIMS) wajen bibiyar ayyukan gwamnati da kuma neman a ɗauki matakan inganta ilimi.

Alausa ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan sauye-sauye a fannin ilimi, ciki har da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inganta ilimin sana’o’i da na kimiyya, da kuma amfani da fasahar zamani wajen koyarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *