Mutane 11 sun rasa ransu sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wani gidan marayu da ke wajen birnin Aljeriya, a safiyar yau Alhamis.
Hukumar kariya ta Farar Hula ta Aljeriya ta ce gobarar ta fara ne kafin wayewar gari, inda jami’an ceto suka isa wurin da misalin ƙarfe 3:00 na safe domin gudanar da aikin kashe wuta da ceto waɗanda abin ya shafa.
Lamarin ya faru ne a wata cibiyar kula da marayu da yara masu buƙatar kulawa ta musamman da ke yankin Mohammadia, a gabashin birnin Aljeriya. Rahotanni sun ce jami’an kashe gobara sun shafe sa’o’i suna ƙoƙarin shawo kan wutar, yayin da har yanzu hukumomi ba su bayyana musabbabin tashin gobarar ba, yayin aikin ceto, jami’an agaji sun samu nasarar fitar da yara biyar masu buƙata ta musamman daga cikin ginin.
- Kotu: Malami ya kasa tabbatar da asalin kuɗin sayen kadarori 48
-
Bayan watanni shida, EFCC ta samu nasarar ƙwace kadarorin da ake alaƙanta da ga Malami
-
Tinubu ya ƙaddamar da rukunin samar da ruwa na Bwari, Ya yi kardadon faɗaɗa samar da ruwa a FCT
Hukumomin Aljeriya ba su fitar da cikakken bayani kan shekarun waɗanda suka rasu ba,wannan mummunan alamarin yafaru ne a daidai lokacin da Aljeriya ke fama da tsananin zafi, lamarin da ya haddasa barkewar gobarar daji kusan 1,000 a faɗin ƙasar cikin makon da ya gabata. Hakan ya ƙara matsin lamba ga jami’an agajin gaggawa da ke ci gaba da fafutukar shawo kan irin waɗannan yanayi.