Wasu ‘yan jarida biyu a Jamhuriyar Nijar sun samu ‘yancin kan su bayan sun shafe kusan watanni takwas a tsare.
Waɗanda aka saki sun haɗa da babban editan shafin labarai na Les Echos du Niger, Youssouf Seriba, da editan jaridar Le Herisson, Oumarou Kane an kama su ne tun watan Nuwamban shekarar 2025.
Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin ‘yan jaridar ya tabbatar da sakin nasu, yana mai cewa sun fito daga gidan yari.
Haka kuma wata majiya daga kotu ta tabbatar da hakan, sai dai ba ta yi karin bayani kan dalilin sakin ba.
An kama ‘yan jaridar ne bayan wata takardar gayyata zuwa taron manema labarai na wata kungiya da gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta kafa domin tara gudummawar jama’a, ta bazu a kafafen sada zumunta.
Rahotanni sun ce magoya bayan shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, sun yi amfani da takardar wajen sukar gwamnatin mulkin soja.
Sai dai har yanzu akwai wani ɗan jarida na uku da aka kama bisa wannan zargi, wanda ke ci gaba da kasancewa a tsare, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2023, wanda ya kifar da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Mohamed Bazoum, kungiyoyin kare hakƙin bil’adama na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ake matsa wa ‘yan jarida da masu fafutukar kare hakƙin jama’a a Nijar.