Cibiyar masu rajin ci gaba ta TPI tare da kungiyar tsofaffin kansiloli ta Najeriya (AFFCN) sun bayyana shirin su na wayar da kan al’ummomin ƙasa baki ɗaya kan gyaran tsarin zaɓe da kuma sauye-sauyen haraji da Gwamnatin Tarayya ta aiwatar.
Babban Daraktan TPI, Dakta Lanre Adebayo ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja.
Adebayo ya ce manufar taron ita ce ta taimaka wa jama’a su fahimci muhimman sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.
- Ɓunƙasa Ilimi da rage talauci: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirye-shirye biyar na bankin Duniya
- WOFAN ta gina gadar tafiyar ƙasa da rijiya ga al’ummar Danbare a Kano
- NDLEA na neman wasu jagororin saida miyagun kwayoyi ruwa a jallo
Ya bayyana cewa za a fara taron a yankin Kudu maso Kudu (South-South) a matsayin gwaji, wanda zai gudana a Uyo, Jihar Akwa Ibom, a ranakun 13 zuwa 14 ga Agusta.
A cewarsa, wannan shiri na wayar da kan jama’a zai magance yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma rashin fahimta game da sauye-sauyen da gwamnati ta kawo.
Ya ƙara da cewa taron zai ƙarfafa shiga cikin harkokin mulki da dimokuraɗiyya tare da ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwa su mallaki manufofin gyaran da gwamnati ke aiwatarwa.
A nasa jawabin, Jami’in Hulɗa na Ƙasa na AFFCN, Nkereuwem James, ya ce ya fi dacewa a wayar da kan jama’a game da waɗannan manufofi maimakon a bar su su ruɗe da bayanan da jam’iyyun adawa ke yaɗawa.