Gobara ta tashi a ɗaya daga cikin tashoshin samar da wutar lantarki da tace ruwan sha na ƙasar Kuwait a ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Kuwait (KUNA) ya wallafa, ma’aikatar ta danganta lamarin da abin da ta bayyana a matsayin “harin ta’addanci da Iran ta kai.”

Ma’aikatar ta ce gobarar ta tilasta ɗaukar matakan kariya na gaggawa wajen gudanar da ayyukan tashar domin tabbatar da tsaron ma’aikatan da kayayyakin aiki, tare da kiyaye daidaiton tsarin samar da wutar lantarki a ƙasar.

Lamarin ya ƙara dagula matsalolin da suka shafi cibiyoyin samar da wutar lantarki da ruwan sha na Kuwait tun bayan ci gaba da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran.

A cikin kwanakin baya, rundunar sojin Kuwait ta ce tana ci gaba da fuskantar barazanar makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙi (drones) da ke shiga sararin samaniyar ƙasar lokaci zuwa lokaci

Hukumomin tsaron sararin samaniyar Kuwait sun ce suna ci gaba da kakkabo duk wasu makamai ko jiragen da ake zargin suna da barazana, yayin da gwamnati ta buƙaci mazauna ƙasar su ci gaba da bin umarnin kariya da hukumomin da abin ya shafa ke bayarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *