Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci a ƙara tsaurara dokokin a harkar haƙar ma’adinai, bayan zaftarewar ƙasa a wani wurin haƙar kwal a Jihar Kogi da ya yi sanadin mutuwar ma’aikata 20.

Matakin ya biyo bayan wani ƙuduri da Sanatan Kogi ta Gabas, Isah Jibrin, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba, inda sanatoci suka yi shiru na minti ɗaya domin girmama waɗanda suka rasu.

Majalisar ta kuma buƙaci Ma’aikatar Ma’adinai ta Tarayya da ta gudanar da bincike a faɗin ƙasar kan masu lasisin haƙar ma’adinai, tare da sanya ido kan ayyukan su domin rage haɗurran da ke faruwa.

Hakazalika, sanatocin sun nemi gwamnatin tarayya ta kafa tsarin diyya ga ma’aikatan haƙar ma’adinai da za a riƙa tallafawa ta hanyar gudummawar kamfanonin da ke da lasisi, domin biyan diyya ga waɗanda suka ji rauni ko suka rasa rayukan su a bakin aiki.

Majlisar, ta kuma umarci Kwamitin ta na Ma’adinai da ya samar da wata doka da ta shafi diyya, tare da bai wa kwamitocin da abin ya shafa wa’adin makonni shida ya gabatar da rahoton sa, domin aiwatar da matakan da aka amince da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *