Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta bayyana shirin ƙaddamar da kuɗi na bai ɗaya na yankin mai suna ECO nan da shekarar 2027, a wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen yankin.
Kuɗin, mai suna ECO, na daga cikin manyan shirye-shiryen ECOWAS na samar da tsarin kuɗi guda wanda zai sauƙaƙa kasuwanci da zuba jari da mu’amalar kuɗi tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka.
A cewar shirin, amfani da kuɗin bai guda zai taimaka wajen rage matsalolin musayar kuɗaɗe daban-daban da ake fuskanta a tsakanin ƙasashe, tare da rage kuɗin gudanar da harkokin kasuwanci da na kuɗi.
- An kunna Na’urorin kariyar sararin samaniya a Tehran
- Yaya aikin shimfida bututun iskar gas daga Najeriya zuwa Morocco yake?
- Takaddama tsakanin Amurka da Iran ta faɗaɗa zuwa ƙasashen Gulf
An tsara ECO ne domin sauƙaƙa kasuwanci tsakanin ƙasashen ECOWAS daa rage kuɗin musayar kuɗaɗe da ƙara zuba jari da ƙarfafa bunƙasar tattalin arzikin yankin. Haka kuma, ana sa ran zai sauƙaƙa tafiye-tafiye da harkokin kasuwanci tare da samar da babbar kasuwa guda mai haɗin kai a Yammacin Afirka.
Ƙasashen ECOWAS da ake sa ran za su shiga tsarin ECO sun haɗa da Najeriya da Ghana da Senegal da Côte d’Ivoire da Benin da Togo da Guinea da Guinea-Bissau da Liberia da Sierra Leone da Gambia da Cape Verde da Burkina Faso da Mali da kuma Nijar.
ECOWAS na shirin aiwatar da tsarin ECO a hankali, inda ƙasashen da suka cika sharuddan tattalin arziki za su fara amfani da kuɗin kafin sauran ƙasashe. Wannan yana nuna cewa ba lallai ne dukkan ƙasashen mambobin ECOWAS su fara amfani da kuɗin a lokaci guda ba.
Masana tattalin arziki na ganin cewa idan aka samu nasarar aiwatar da shirin, ECO zai iya taimakawa wajen ƙarfafa kasuwancin cikin gida na yankin, rage dogaro da musayar kuɗaɗe na ƙasashen waje, da kuma ƙara haɗin kan tattalin arzikin Yammacin Afirka.
Sai dai akwai ƙalubale da suka haɗa da bambancin manufofin tattalin arziki, hauhawar farashi, basussukan gwamnati, da rashin daidaiton tattalin arzikin ƙasashe mambobi, waɗanda za su iya shafar lokacin fara amfani da kuɗin.
A halin yanzu, ECOWAS na ci gaba da aiki tare da ƙasashe mambobi domin ganin an cika sharuddan da suka dace kafin fara amfani da kuɗin ECO.