Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka, CAF, Patrice Motsepe, ya ce rashin Najeriya da Kamaru a Gasar cin Kofin Duniya ta 2026 babban hasara ne ga ƙwallon ƙafa ta Afirka.
Ya jaddada cewa gasar ta duniya ba ta cika ba ba tare da ƙasashen biyu mafi nasara a nahiyar Afirka ba.
Najeriya da Kamaru ba su samu tikitin shiga Gasar cin Kofin Duniya ta 2026 ba, wcce ƙasar Spaniya ta lashe kofin.
-
Super Falcons za ta samu dala miliyan 2 idan ta…
-
Barcelona ta sayi Adeyemi daga Dortmund
-
Ana sa ran Klopp ya zama sabon Kocin Jamus
“Ina ci gaba da cewa Gasar cin Kofin Duniya ba tare da Najeriya da Kamaru da sauran su ba, ba cikakkiya ba ce, domin ‘yan Najeriya da ‘yan Kamaru sune abun alfaharin mu,” in ji Motsepe.
Yayin da yake magana kan ƙoƙarin Afirka a gasar, Motsepe ya ce Najeriya da Kamaru sun taka muhimmiyar rawa wajen kafa tarihi ga nahiyar a fagen ƙasa da ƙasa. Ya kuma bayyana aniyarsa ta ganin an ƙara yawan ƙasashen Afirka da za su samu shiga gasar a gaba.
Duk da ya yaba da nasarar Moroko da Masar a gasar Kofin Duniya ta 2026, Motsepe ya ce kowacce ƙasa ta bayar da gudunmawar ci gaban ƙwallon ƙafa a Afirka, musamman manyan ƙasashe irin su Najeriya da Kamaru, waɗanda kasancewarsu ke ƙara wa Gasar cin Kofin Duniya daraja da sha’awa.
