Babbar Kotun Afrika ta Kudu ta bayar da umarnin wucin gadi a ranar Juma’a wanda ya dakatar da shirin Majalisar Dokoki na gudanar da binciken tsige Shugaba Cyril Ramaphosa

Ramaphosa ya nemi kotun ta dakatar da binciken har sai an kammala nazarin shari’a kan rahoton wani kwamitin bincike mai zaman kansa da aka fitar a shekarar 2022

Rahoton ya nuna cewa mai yiwuwa shugaban ya karya kundin tsarin mulkin ƙasar, kuma akwai hujjojin da za su sa ya amsa tambayoyi kan abin da ake kira badakalar “Farmgate.”

Badakalar ta shafi satar dala 580,000 na Amurka a shekarar 2020, da wasu kuɗaɗen waje da ba a bayyana su ba, waɗanda aka ɓoye a cikin kujera a gonar kiwon namun dajin Phala Phala ta Ramaphosa da ke lardin Limpopo

Sai dai Ramaphosa ya musanta aikata wani laifi, yana mai cewa kuɗaɗen da aka samu ne daga sayar da bafulo, sannan ya ce ba zai yi murabus saboda wannan batu ba

Sai dai a watan Mayun wannan shekara, Kotun Tsarin Mulki ta soke matakin majalisar, lamarin da ya haifar da kafa kwamitin majalisa domin gudanar da binciken yiwuwar tsige shugaban

Hukuncin da kotun ta yanke na wucin gadi na nufin Ramaphosa zai kauce wa ƙarin matsin lamba da kunya da ke tattare da badaƙalar har sai an saurari ƙarar nazarin rahoton

Idan aka ci gaba da shirin tsige shi, zai kasance karo na farko da aka fara irin wannan tsari kan shugaban ƙasa mai ci a Afrika ta Kudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *