Tawagar ‘yan wasan ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya, Super Falcons, ta fitar da sabuwar rigarta gabannin fara Gasar cin Kofin Mata ta nahiyar Afirka, WAFCON ta 2026.
Sabuwar rigar mai launin kore, tana ɗauke da taurari 10 a kusa da tambarin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF).
Kowanne tauraro na nufin kowacce gasar WAFCON da Najeriya ta lashe tun daga shekarar 1998 zuwa 2024.
Najeriya ta fara sanya sabuwar rigar ne a wasan sada zumunta da ta doke Tanzania da ci 2-1 a ranar 23 ga Yuli, kafin gasar nahiyar ta fara.
-
Gwamna Sule ya bai wa Nasarawa Amazons da sauran ƙungiyoyin wasanni kyautar kuɗi da mota
-
Gwamnatin Tarayya ta baiwa tawagar ‘yan wasan ɗaga nauyi na masu buƙata ta musamman kyautar kuɗaɗe
-
Super Falcons za ta fara kare kambunta na WAFCON akan Malawi ranar Lahadi
Super Falcons na ci gaba da zama tawagar mata mafi nasara a Afirka, inda ta lashe kofuna 10 na nahiyar.
Sabuwar rigar ta Super Falcons tana kuma nuna burin tawagar na lashe kofin WAFCON na 11 a wannan bazara idan suka yi nasara a Moroko, kazalika zai taimaka mata wajen shirye-shiryen neman tikitin shiga gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027.
